Buhari ya kaddamar da ayyuka a Imo

36

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa Owerri, babban birnin jihar Imo inda ya kaddamar da wasu ayyukan da gwamnan jihar Hope Uzodinma ya aiwatar cikin watanni 32 na gwamnatinsa.

Jirgin shugaban kasar ya sauka a filin jirgin saman kaya na kasa da kasa na Sam Mbakwe dake birnin Owerri da misalin karfe 10 da mintuna 46 na safe.

Shugaban kasar da ‘yan tawagarsa sun samu tarba daga gwamnan wanda yazo tare da jiga-jigan gwamnatin jihar.

Kazalika, a filin jirgin sama domin tarbar shugaban kasar akwai wasu manyan jami’an tsaro da shugabannin jam’iyyar APC a jihar da na yankin kudu maso gabas.

Bayan saukarsa, shugaban kasar ya duba faretin ban girma da sojojin Najeriya suka yi masa.

Kazalika ya kalli wasannin gargajiya wanda hukumar kula da wasanni da al’adu ta jihar Imo ta shirya masa.

Shugaba Buhari daga baya ya kaddamar da titin Orlu zuwa Owerri mai nisan kilomita 35 da titin Owerri zuwa Okigwe mai nisan kilomita 48 tare da ginin majalisar dokokin jihar da aka gyara, da sauran ayyuka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen − 7 =