Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ya dage fara yakin neman zaben da aka shirya farawa a gobe.
Daraktan yada labarai na kwamitin, Bayo Onanuga a wata sanarwa da ya fitar jiya ya ce kwamitin zai fara yakin neman zabe gobe tare da gudanar da taron addu’o’i da kuma tattakin zaman lafiya a Abuja, daidai da jadawalin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na shekarar 2023.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar yau a Abuja, babban daraktan yakin neman zaben Tinubu/Shettima kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya sanar da dage yakin neman zaben yana mai cewa an dage ne domin a samar da damar shigar da wasu jiga-jigan jam’iyyar a kwamitin.
A cewar Simon Lalong, saboda kara yawan sunayen ‘yan kwamitin, domin samun karin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC, sun yanke shawarar dage fara yakin neman zaben domin tabbatar da cewa an shigar da kowa da kowa kafin a fara.
Sanarwar ta kara da cewa za a sanar da sabuwar ranar fara yakin neman zaben nan ba da jimawa ba.