An rantsar da William Ruto a matsayin shugaban Kenya

42

Dubun dubatar jama’a ne suka yi ta murna yayin da aka rantsar da William Ruto a matsayin shugaban kasar Kenya a wani biki da aka gudanar a Nairobi babban birnin kasar bayan da ya lashe zaben da aka yi a watan jiya.

William Ruto ya yaba da lokacin da babu kamarsa, ya kara da cewa dan kauye ya zama shugaban kasa.

Dan takarar da ya sha kaye Raila Odinga bai halarci taron ba. Ya ce yana da matukar damuwa game da nasarar da abokin hamayyarsa ya samu.

William Ruto ne ya lashe zaben da kashi 50.5 na kuri’un da aka kada, inda ya doke Raila Odinga wanda ya samu kashi 48.8.

Raila Odinga ya yi zargin cewa an tabka magudi a sakamakon zaben, amma kotun kolin kasar ta ce an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.

An mika wa William Ruto, tsohon mataimakin shugaban kasar kwafin kundin tsarin mulkin kasar Kenya da takobi daga tsohon shugaban kasar Uhuru Kenyatta.

Dauke da Bible a hannunsa, dan shekara 55 din ya yi rantsuwa cewa zai kiyaye da kuma kare tsarin mulkin kasar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 − four =