Ambaliyar ruwa na yiwa garin Hadejia barazana a Jigawa

343

A halin da ake ciki yanzu haka, ambaliyar ruwa na barazanar shiga garin Hadejia da ke karamar hukumar Hadejia a jihar Jigawa.

Hakan yazo ne bayan da ruwa ya ballo daga kogin Dole tare da haura jingar da aka yi daga unguwar Garko zuwa Fantai cikin birnin da tsakar daren jiya.

Shugaban karamar hukumar Hadejia, Abdulkadir Bala Umar T.O ya umarci masallatai su yi kiran sallah da misalin karfe 12 zuwa 1 na dare domin ankarar da mutane tare da neman su fito wajen aikin jinga.

Dalilin haka mutane dayawa suka fito cikin daren kuma aka cigaba da kokarin gyara jingar domin kare ruwan daga shigowa cikin gari.

Majalisar karamar hukumar da daidaikun mutane har da wasu kungiyoyi da hukumomi sun bayar da gudunmawar fatar buhuna domin cigaba da aikin jingar.

Tuni dai ambaliyar ruwan ta tashi kauyuka da dama a yankin, lamarin da ya sanya mutanen kauyukan suka yi gudun hijira zuwa sansanoni da gidajen ‘yan’uwa dake cikin garuruwa daban-daban mafi kusa da su.

Ambaliyar ta bana ta kuma lalata gonaki da dama tare da jawo asarar rayuka dayawa a yankin na kasar Hadejia da ma jihar Jigawa baki daya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 − thirteen =