‘Yan sanda a birnin Kabul na kasar Afganistan sun ce wani harin kunar bakin wake da aka kai a wata cibiyar koyar da karatu a birnin ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 19 tare da jikkata wasu da dama.
Fashewar ta faru ne a cibiyar ilimi ta Kaaji da ke yammacin birnin.
Jami’ai daga cibiyar sun ce dalibai na gudanar da jarabawar gwaji ta jami’a.
Yawancin wadanda ke zaune a yankin sun fito ne daga kananan kabilun Hazara, wadanda aka kai hare-hare a baya.
Hotunan da aka nuna a gidan talabijin, wadanda kuma aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna cikin wani asibiti da ke kusa, inda aka shimfida gawarwaki a kasa.
Cibiyar karantarwa ta Kaaji mai zaman kanta ce, wacce ke koyar da dalibai maza da mata. An rufe galibin makarantun ‘yan mata a kasar tun bayan da kungiyar Taliban ta koma kan karagar mulki a watan Agustan bara, amma wasu makarantu masu zaman kansu suna bude.
Har yanzu dai babu wata kungiya da ta bayyana cewa ita ce ta kai harin.