Hukumar kare hakkin mai saye ta tarayya ta ce yankewa mutum wutar lantarki ba tare da bashi wa’adin kwanaki 10 ba, farawa daga ranar da aka ba shi takardar biyan kudin wuta, ya sabawa tanadin doka.
Mataimakin shugaban hukumar, Babatunde Irukera ne ya bayyana haka jiya, a Calabar, babban birnin jihar Cross Rivers, a wani dandalin warware korafe-korafen masu amfani da wutar lantarki.
Babatunde Irukera ya koka bisa yadda kamfanin rarraba wutar lantarki na Fatakwal ke ayyukansa a birnin Calabar da kewaye.
Ya ce daga binciken da hukumar ta gudanar, kamfanin rarraba wutar lantarkin bai taka rawar gani ba, wajen samar da wutar lantarki ga masu amfani da ita, bisa la’akari da kudaden da suke biya.
Babatunde Irukera ya ce rahotannin da suka samu kan ayyuka da dama na kamfanin sun hada da yanke wutar lantarkin mutane da kamfanin ya yi ba tare da bin doka ba.