‘Yan takarar jam’iyyar APC kadai zan goyawa baya – Buhari

45

Gabanin zaben 2023, shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya ce ba zai goyi bayan ‘yan takarar wasu jam’iyyun siyasa ba, sai na jam’iyyar sa ta APC.

Bayanin shugaban kasar ya zo ne a daidai lokacin da ake ta yada jita-jitar cewa wasu jiga-jigan jam’iyya mai mulki za su marawa dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar baya a kan Bola Tinubu, takwaransa na APC.

Shugaba Buhari, a cewar wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar, ya ce zai goyi bayan ‘yan takarar da jam’iyyar APC ta tsayar a zabe mai zuwa.

Garba Shehu ya ce shugaban kasar ya ba da tabbacin cewa zai ci gaba da marawa jam’iyyar baya a dukkan matakai domin tabbatar da da’a, aiki tare da hada kai.

Ya kuma kara da cewa, shugaba Buhari ya umarci jami’an dake fadar shugaban kasa da kewaye da kuma duk masu shiga tsakani da su guji furta kalamai masu janyo cece-kuce, wanda a karshe zasu cutar da jam’iyya da kuma gwamnati.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 + 8 =