Tsohon mataimakin shugaban kungiyar al-Shabab ya zama minista a Somalia

65

An nada tsohon mataimakin shugaba kuma mai magana da yawun kungiyar al-Shabab ta Somaliya a matsayin ministan gwamnati.

An zabi Mukhtar Robow a matsayin ministan harkokin addini a sabuwar majalisar ministocin kasar Somaliya.

Ya shafe shekaru hudu yana kulle a gidan yari bayan tsare shi a mulkin tsohon shugaban kasar bisa laifin shirya kungiyar ‘yan bindiga. An kuma zarge shi da kin watsi da tsattsauran ra’ayi.

Fiye da mutane 20 ne suka mutu lokacin da rikici ya barke bayan kama shi.

A shekara ta 2015 ne ya fice daga kungiyar al-Shabab saboda bambance-bambancen akida, inda ya kafa kungiyarsa ta masu fafutuka.

A baya Amurka ta sanya sunansa a cikin jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo, ta yi tayin bayar da kyautar dala miliyan 5 don kama shi, amma an yi watsi da hakan a shekarar 2017.

Nadin da aka yi masa a matsayin ministan harkokin addini na iya nufin matakin ayyana yakin akida da kungiyar al-Shabab.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + one =