Tsawa ta kashe wata yarinya mai shekara 12 a Jigawa

71

Tsawa ta kashe wata yarinya ‘yar shekara 12 mai suna Maryam Rabi’u Garba a karamar hukumar Kaugama ta jihar Jigawa.

Wani mazaunin karamar hukumar ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da yarinyar ke fakewa a wani aji sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Ya ce yarinyar za ta koma gida ne bayan mahaifiyarta ta aike ta zuwa wani waje.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Dutse, babban birnin jiha.

Ya ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya a garin Kaugama.

Ya ce an garzaya da yarinyar zuwa asibiti kuma likita ne ya tabbatar da mutuwarta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 + nine =