
Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa uku da suka hada da wani babban kwamandan ‘yan rajin kare kai, Ibrahim al-Nabulsi a wani samame da suka kai birnin Nablus da ke yammacin gabar kogin Jordan.
A cewar ma’aikatar lafiya ta Falasdinu, sojojin Isra’ila sun yi wa wani gini kawanya da misalin karfe 5 na safe agogon kasar a yau, inda Ibrahim al-Nabulsi, kwamandan mayakan kare masallacin Qudus, ya kebe kansa a ciki.
An kwashe sa’o’i da dama ana musayar wuta da bindigogi.
Ma’aikatar lafiya ta kasar ta ce an kashe Ibrahim Al-Nabulsi mai shekaru 30 tare da Islam Sabbouh mai shekaru 32 da Hussein Jamal Taha, inda ta kara da cewa wasu mutane fiye da 60 sun samu raunuka yayin da hudu ke cikin mawuyacin hali.
Masu aiko da rahotanni sun ce Ibrahim al-Nabulsi ya ki mika wuya, kuma wasu Falasdinawa dauke da makamai sun kare shi kafin a kashe shi.
Ibrahim Al-Nabulsi, wanda aka fi sani da zakin Nablus, ya shafe watanni da dama yana buya, kuma ya sha tsallake rijiya da baya a yunkurin kashe shi da Isra’ila ke yi.