Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya da kungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya domin dakile tashe-tashen hankulan addini a kasar gabanin babban zaben 2023.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a yayin taron ‘yancin addini na kasa da kasa wanda Gidauniyar Zaman Lafiya ta Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil’adama na duniya guda 70 suka shirya a birnin Washington D.C na kasar Amurka.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun tsohon shugaban kungiyar ta CAN, Reverend Samson Ayokunle, wacce ya fitar jiya a Abuja.
A cewarsa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Dr Saad Abubakar, wanda kuma shine shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta Najeriya, ya samu wakilcin Farfesa Yusuf Usman, tsohon babban sakataren hukumar inshorar lafiya ta kasa.
Samson Ayokunle ya ce kungiyoyin biyu sun amince da karfafawa musulmi da kiristoci a kasarnan gwiwa akan su guji tashin hankali da rungumar tattaunawa da kuma jajircewa wajen gina al’ummomin dake rayuwa cikin zaman lafiya da lumana.