Nijar ta fara amfani da fasahar samar da ruwan sama domin dakile fari

60

Jamhuriyar Nijar ta fara amfani da fasahar samar da ruwan sama da nufin rage illar fari a kasar.

Hukumomin yanayi na kasar ne suka bayyana hakan a jiya.

Kasar wacce yawancinta sahara ce ta fuskanci matsalar karancin abinci tsawon shekaru saboda karancin ruwan sama.

Shugabar cibiyar nazarin yanayi ta kasar, Katiellou Gaptia Lawan, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa dole ne gwamnati ta yi wani abu game da fari.

Fasahar samar da ruwan sama ta hada da amfani da jirgin sama domin fesa sinadarai cikin gajimare.

Za ayi amfani da fasahar ne a a guraren da ake samun gonakin da mutane ke nomawa.

Wasu sassan kasar sun fuskanci ambaliyar ruwa, lamarin da ya kara tabarbarewar karancin abinci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + twenty =