NDLEA ta kama dagaci a Sokoto da laifin safarar miyagun kwayoyi

38

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, reshen jihar Sokoto, ta cafke wani da ake zargin dillalin kwayoyi mai suna Umar Mohammed, dagacin kauyen Ruga da ke karamar hukumar Shagari a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai jiya a Sokoto, kwamandan NDLEA a jihar, Adamu Iro, ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan binciken sirri da hukumar ta gudanar.

Adamu Iro ya ce wanda ake zargin, wanda ya kasance mai rike da sarautar gargajiya ya dade a jerin sunayen wadanda hukumar ke zargi da safarar miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa tuni wanda ake zargin ya amince da aikata laifin tare da sanar da hukumar cewa ya dade yana sana’ar.

Ya ce rundunar za ta tabbatar da aiwatar da abinda ya dace, amma za a gaggauta gudanar da bincike kan lamarin domin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Kwamandan ya kuma baiwa ‘yan kasarnan tabbacin cewa hukumar NDLEA ta kuduri aniyar kai samame a wuraren da masu safarar miyagun kwayoyi ke hada-hada, tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban kuliya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × five =