Mutane miliyan 1 sun tsere daga gidajensu saboda fari a Somalia – MDD

42

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fari mafi muni da Somaliya ta fuskanta cikin shekaru 40 da suka gabata, ya raba mutane miliyan daya da muhallansu tare da jefa kasar cikin mawuyacin hali na yunwa.

Fiye da kashi uku bisa hudu na mutanen miliyan daya ‘yan gudun hijira ne a kasarsu.

Damuna hudu da babu ruwan sama ya jawo lalacewar amfanin gona da mutuwar dabbobi, kuma damina ta biyar mara ruwan sama da ake tsammani za ta raba karin wasu mutane da yawa da muhallansu.

Daraktan hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasar Norway Mohammed Abdi, ya ce adadin na mutane miliyan daya ya kasance babbar alamar tashin hankali ga Somalia.

Ya ce wasu iyalai sun gudu sun bar kayansu gabadaya domin a zahiri babu ruwa ko abinci da ya rage a kauyukansu.

Mohammed Abdi ya kuma yi kira da a ba da tallafin gaggawa tun kafin lokaci ya kure.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 + 1 =