Mali ta zargi Faransa da aikawa da makamai ga masu tayar da kayar baya

81

Dangantaka tsakanin Faransa da Mali dai na ci gaba da tabarbarewa, inda kasar Mali ta zargi kasar da ta yi mata mulkin mallaka, Faransa, da bayar da makamai da bayanan sirri ga masu adawa da gwamnati.

A wata wasika da ya aike wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye Diop, ya ce Faransa ta keta sararin samaniyar Mali a lokuta da dama tare da kai makamai ga mayakan a wani yunkuri na tada zaune tsaye a kasarsa.

Faransa ta yi watsi da zargin.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta lalace ne biyo bayan juyin mulkin da aka yi har sau biyu da kuma shawarar da shugabannin sojojin Mali suka yanke na yin aiki kafada da kafada da sojojin haya daga kasar Rasha.

A ranar Lahadin da ta gabata ne Faransa ta ce a halin yanzu dukkan sojojinta sun fice daga kasar Mali, inda suka kwashe kusan shekaru 10 suna yaki da mayaka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + ten =