Majalisar wakilai ta gayyaci ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Hajiya Zainab Ahmed, domin ta gabatar da takardu da suka shafi batun tallafin man fetur daga shekarar 2013 zuwa yau.
Ibrahim Aliyu, shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar na musamman da ke binciken tsarin tallafin man fetur ne ya bayyana hakan a lokacin da Stephen Okon, Daraktan kudi na ma’aikatar ya bayyana a gaban kwamitin jiya a Abuja.
Shugaban kwamitin ya baiwa ministar nan da ranar 16 ga watan Agusta ta bayyana a gabansa, da duk wasu takardun da suka dace wadanda suka shafi tallafin man fetur.
Shugaban kwamitin ya ce dole ne ministar tayi bayani akan jimillar kudaden da aka fitar daga asusun ajiyar kudaden shiga a matsayin biyan tallafin man daga shekarar 2013 zuwa yau.
Ya ce dole ne a gabatarwa da kwamitin da sunayen kamfanonin da suka ci gajiyar kudaden tallafin daga asusun tattara kudaden shiga.