
Majalisar dokokin jihar Kano a jiya ta tantance tare da tabbatar da nadin kwamishinoni guda tara da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mika mata sunayensu.
An tantance su yayin zaman majalisar wanda kakinta, Hamisu Ibrahim-Chidari ya jagoranta.
Tun da farko dai kakakin majalisar ya sanar da karbar wasikar Gwamna Ganduje ta neman karin sunan Dakta Aminu Ibrahim-Tsanyawa domin tantance shi a matsayin kwamishina.
Sabbin kwamishinonin sun hada da Ibrahim Dan’azumi da Abdulhalim Abdullahi da Lamin Sani-Zawiyya da Ya’u Abdullahi-Yan’shana da Garba Yusuf Abubakar da Dr Yusuf Jibirin.
Sauran sun hada da Adamu Fanda da Saleh Kausami da Dr Ali Burum-Burum.
Kakakin majalisar ya ce an aika wa Ibrahim-Tsanyawa takardar gayyatarsa ya bayyana a gaban majalisar a yau domin tantance shi.