
Shugabannin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa sun ce kungiyar ta dakatar da yajin aikin da ta shiga.
Dakatarwar ta tsawon makonni biyu ce.
Shugaban kungiyar reshen babban birnin tarayya, Godfrey Abah ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran na kasa jiya a Abuja.
Godfrey Abah ya ce dakatarwar ta biyo bayan ganawar da suka yi da Ministan Kwadago, Chris Ngige, da Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu, da kuma Karamin Ministan Wutar Lantarki, Goddy Jedy-Agba, da wakilin Shugaban Ma’aikata.
Yace sauran wadanda suka halarci zaman ganawar sun hada da wakilin ofishin sayar da kadarorin gwamnati da kuma shugabannin kamfanin watsa wutar lantarki na kasa, TCN.
Ya ce an gabatar da dukkan batutuwan da ake kiki-kaka akai, kuma an kafa wata tawaga mai karfi da za ta binciki lamarin tare da bayar da rahoto cikin makonni biyu.