Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, Buba Marwa, ya ce jihar Legas ce take da kashi 33 cikin 100 na masu shan muggan kwayoyi a kasar nan.
Buba Marwa ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma a fadar Sarkin Badagry, Aholu Menu-Toyi, a Legas.
A cewarsa, adadin na kashi 33 cikin 100 yana da yawa kuma shine mafi girma a kasarnan.
Ya yabawa kokarin Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas wajen taimakawa hukumar yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Da yake mayar da martani, Sarkin na Badagry ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa hukumar wajen magance shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Basaraken ya yabawa Buba Marwa kan yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi ba sani ba sabo.
Ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da yi masa jagora a kokarinsa na kawar da fataucin miyagun kwayoyi a kasar nan.