
Shugabannin kungiyar ‘yan kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo sun ce kungiyar tana goyon bayan yunkurin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Kungiyar ta zayyano dalilanta ne kan karuwar rashin tsaro da ya daidaita kasarnan.
Kungiyar ta ce sace mutane, da kashe ‘yan Najeriya ciki har da jami’an tsaro na babbar barazana ga rayuwar al’ummar kasarnan.
Sakatare-Janar na kungiyar ta Ohanaeze Ndigbo, Mazi Okechukwu Isiguzoro, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau.
Isiguzoro, ya yabawa mambobin jam’iyyar adawa a majalisun kasarnan kan daukar irin wannan matakin da ya dace.
Ko da yake, lsiguzoro wanda ya ce ‘yan kabilar Igbo sun dauki sanarwar tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin kokarin farkar da shugaban kasar, ya bayar da shawarar cewa a cigaba da shirye-shiryen tsige shi idan shugaban kasar ya ki canjawa.
A wani batun kuma, sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa a jam’iyyar APC, Adamu Bulkachuwa, ya goyi bayan matakin da wasu ‘yan majalisar kasarnan suka dauka na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda tabarbarewar tsaro a kasarnan.
An bayyana cewa Adamu Bulakchuwa shi ne sanata na biyu a jam’iyyar da ke goyon bayan yunkurin tsige shi bayan Elisha Abbo na jihar Adamawa.
Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Yuli ne sanatocin jam’iyyun adawa a zauren majalisar suka ba wa shugaban kasar wa’adin makonni shida da ya magance rashin tsaro a kasarnan ko kuma a tsige shi.
Da yake bayyana dalilansa na goyon bayan yunkurin tsige shi a wata hira da gidan talabijin na Channels, Adamu Bulkachuwa ya ce tsige shugaban kasar shi ne zabi na karshe da ya rage wa ‘yan majalisar bayan kokarin da suka yi na taimakawa shugaban kasar wajen magance matsalar rashin tsaro ya ci tura.
Adamu Bulakchuwa ya kuma bayyana cewa da yawa daga cikin ‘yan majalisar na jam’iyyar APC sun goyi bayan shirin a lokacin da aka tabo batun a wata ganawar sirri da suka yi.