Kungiyar Next Jigawa ta nemi ‘yan Jigawa su zabi sahihan ‘yan takara

66

Kungiyar Next Jigawa ta bukaci al’ummar jihar da su zabi sahihin dan takara da ya damu da ci gaban jihar a zaben 2023 mai zuwa.

Shugaban kungiyar Farfesa Usman Haruna ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake gabatar da takardar bukatar al’umma ga ‘yan takarar gwamna na jam’iyyun siyasa hudu na APC da NNPP da PDP da LP a jihar Jigawa.

Ya ce, kungiyar ta kunshi ’yan kasa, malamai, masu yi wa kasa hidima da wadanda suka yi ritaya, da sauran kungiyoyin kwararru da suka nuna matukar damuwa da ci gaban jihar Jigawa.

Farfesa Usman yace makasudin kafa wannan kungiya shi ne ta hada da jagororin jihar Jigawa a kowane mataki domin yin ayyuka daidai da bukatun ‘yan jiha, ta yadda jihar za ta samu ci gaba ta fuskar zamantakewa, tattalin arziki, da sauran abubuwan da suka shafi rayuwar dan Adam.

Ya ce takardar ta kunshi dukkan bukatun ‘yan jihar Jigawa wadanda za su zama wani tsari ko jagora ga wanda zai shugabanci jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 − eight =