Kungiyar NAAT ta janye yajin aiki

40

Kungiyar malaman fasahar kere-kere ta kasa ta dakatar da yajin aikinta na tsawon watanni shida da take yi saboda rashin aiwatar da yarjejeniyar da ta kulla da gwamnatin tarayya a shekarar 2009.

Shugaban kungiyar na kasa, Ibeji Nwokoma, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a sakatariyar kungiyar ta kasa jiya a Abuja, ya ce dakatarwar ta watanni uku ce kacal.

Ibeji Nwokoma ya ce kafin kungiyar ta fara yajin aikin, an rubuta wasiku da dama zuwa ga Ministocin Ilimi da na Kwadago da Samar da Aikin Yi inda aka bayyana matsalolin kungiyar da kuma bukatar a magance su.

Shugaban kungiyar na kasa ya bayyana cewa, a lokacin yajin aikin, kungiyar ta gudanar da tarurruka da dama da wakilan gwamnati, wadanda suka hada da ministan kwadago da samar da aikin yi, Dakta Chris Ngige.

Ya ce kungiyar, bayan wata kwakkwarar hulda da gwamnati ta samu damar cimma matsaya da kudurori kan wasu bukatunta, duk da cewa ta ki amincewa da kudirin gwamnatin tarayya na ‘babu aiki, babu biya’.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − 16 =