Hukumar kula da yanayi ta yi hasashen ambaliya a jihohi da dama

125

Hukumar Kula da Yanayi ta kasa (NiMET) a jiya ta yi hasashen za a fuskanci ambaliyar ruwa a wasu sassan jihohin Kaduna, Borno, Delta da Bayelsa daga yanzu zuwa watan Oktoban bana.

Haka kuma ta ce ana sa ran samun ruwan sama fiye da yadda aka saba a jihohin Arewa irin su Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Bauchi, Kebbi da Gombe, da kuma arewacin Kaduna da Adamawa cikin watanni uku masu zuwa.

Darakta Janar na hukumar, Farfesa Mansur Matazu, yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya kuma ce wasu sassan jihohin Zamfara, Yobe, Taraba, Borno da Kaduna na iya fuskantar matsakaiciyar barazanar ambaliya.

Mansur Matazu ya yi nuni da cewa lamarin na iya haifar da ambaliya a irin wadannan wuraren idan ba a gyara magudanan ruwa yadda ya kamata ba.

Bugu da kari kuma, hasashen hukumar ya nuna cewa ana sa ran samun ruwan saman kamar yadda aka saba a jihohin tsakiyar kasarnan, da mafi yawan sassan jihohin Kaduna, Adamawa, Edo, Ekiti, Oyo, wasu sassan jihohin Bauchi, Gombe da kuma Ondo.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − 15 =