
Gwamnatin tarayya ta raba naira biliyan 100 ga masu sana’ar sayar da magunguna da masu zuba jari a fannin kiwon lafiya a matsayin lamuni don fadada jarin su, da kuma bunkasa samar da magunguna a cikin kasa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da ya karbi bakuncin sabbin shugabannin kungiyar likitocin Najeriya a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Ya bayyana cewa an bayar da lamunin ne karkashin tallafin da Babban Bankin Kasa CBN ke baiwa kamfanoni masu zaman kansu.
A cewarsa, kwamitin kawo sauyi a fannin kiwon lafiya karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, a halin yanzu yana lalubo hanyoyin farfado da tsarin kiwon lafiyar kasar nan.
Ya bukaci kungiyar da sauran masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya da su goyi bayan shirye-shiryen gwamnatin tarayya.
Shugaba Buhari ya kuma bukace su da su yi aiki tare da kwamitocin da aka kafa domin tsara kiwon lafiya wanda ya fi dacewa da bukatun ‘yan Najeriya a karni na 21.