Gwamnatin tarayya ta horas masu kiwon kaji 360 a jihohi 12

49

Gwamnatin tarayya ta horar da bayar da jari ga masu kiwon kaji 360 a jihohi 12 na tarayyar kasar nan.

Malam Abubakar Bello, daga ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta tarayya, wanda ya jagoranci aikin a jihar Jigawa, ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa a Dutse, babban birnin jihar.

Abubakar Bello ya ce an zabo masu kiwon kaji 30-30 daga jihohi 12 da suka hada da Jigawa domin cin gajiyar wannan shirin.

Ya bayyana cewa a karshen shirin na kwanaki biyu, wanda aka fara a ranar Litinin, za a bai wa kowanne daga cikin wadanda aka horas kaji ‘yan kwanaki 100 a duniya, da buhu biyu na abincin kaji mai nauyin kilogiram 25, da kwanakan ci guda 2 da na sha guda 2 da kuma alluran rigakafi.

Jagoran ya kara da cewa za a ba wa kowanne daga cikin wadanda aka horar kudi domin kai kayayyakin zuwa karamar hukumarsa.

A cewar sa, an dauki wannan matakin da nufin rage talauci da rashin aikin yi a tsakanin ‘yan Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen + eight =