Gwamnatin tarayya ta kulla yarjejeniya da kasar Amurka dangane da dawo da wasu kudaden iyalan Sani Abacha.
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a jiya a Abuja, ya sanya hannu kan yarjejeniyar dawo da kudaden da kuma sarrafa su.
Abubakar Malami ya ce kudaden satar sun kai dala miliyan 23 da dubu 439 da 724, kwatankwacin naira miliyan dubu 9 da miliyan 873.
Ya yi nuni da cewa, tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da a yi amfani da kudaden wajen gudanar da ayyukan shugaban kasa na samar da gine-gine da ababen more rayuwa.
Jakadiyar Amurka a Najeriya Mary Leonard a nata jawabin ta ce Amurka ta kwace wadannan kudade ne a matsayin martani ga Janar Abacha da mukarrabansa da suka saba dokokin Amurka ta hanyar karkatar da kudaden ta kasar Amurka zuwa asusun bakuna a kasar Birtaniya.