Gwamnatin kasar Mali ta nada sabon firaminista na wucin gadi, yayin da rahotanni ke cewa an kwantar fira-minista kuma da dan siyasar farar hula Choguel Maiga a asibiti.
Sabon Firayim Minista, Kanar Abdoulaye Maiga, ya taba zama ministan kula da yankuna da kuma kakakin gwamnati.
A farkon watan Agusta an samu rahoton cewa Choguel Maiga ya yi fama da shanyewar jiki, amma daya daga cikin hadimansa ya musanta hakan.
Abdoulaye Maiga dai ya kasance mai sukar lamirin tsohuwar kasar da ta yiwa Mali mulkin mallaka wato Faransa, inda ya zargi gwamnatin Faransa da assasa sabon tsarin mulkin mallaka da kuma goyon bayan rashin tsaro da rikicin dimokuradiyyar Mali.
Sojoji sun kwace mulki a shekarar 2021, inda suka nada Kanar Assimi Goïta a matsayin shugaban kasar.
Nadin Kanal Abdoulaye Maiga na nufin cewa a halin yanzu manyan mukaman gwamnatin kasar Mali biyu na hannun sojoji.