Gwamnatin Katsina ta mayar da dubban ‘yan gudun hijira zuwa garinsu

40

Gwamnatin jihar Katsina ta mayar da ‘yan gudun hijira sama da dubu 12 da suka hada da mata da kananan yara zuwa kauyensu mai suna Shimfida, dake karamar hukumar Jibia.

An kai mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa garin nasu cikin tsauraran matakan tsaro.

Tun a ranar 10 ga watan Maris aka tarwatsa mutanen kauyen bayan janyewar jami’an soji daga yankin ba zato ba tsammani, wanda ya kai ga kai hare-hare ba kakkautawa daga ‘yan ta’adda tare da halaka mutane da dama.

Kafin mayar da su, sama da mutane dubu 6 ne ‘yan gudun hijira suka yi sansani a makarantar sakandiren ‘yan mata ta gwamnati da ke Jibia, wadanda gwamnatin jihar da kuma majalisar karamar hukumar suka ajiye su, yayin da wasu da suka tsere zuwa makwabciyar jamhuriyar Nijar aka dawo da su Jibia a jiya.

Shugaban majalisar karamar hukumar, Bishir Sabi’u, ya ce kafin a dawo da ‘yan gudun hijirar gwamnan jihar ya tattauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma an ba shi tabbacin samun isasshen tsaro.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + 14 =