Gwamnatin Borno ta rufe hedikwatar NNPP

61

Gwamnatin jihar Borno ta rufe hedikwatar jam’iyyar NNPP ta jihar da ke Maiduguri, babban birnin jihar.

Hukumar raya birane ta jihar Borno ta rufe hedikwatar jam’iyyar tare da wasu ofisoshinta a yau.

Dan takarar gwamnan jihar Borno a karkashin jam’iyyar NNPP, Dakta Umaru Alkali, ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri.

Ya kara da cewa an kama dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar, Attom Muhammad Maigira, bayan ya amsa gayyatar da ‘yan sanda suka yi masa, kuma a halin yanzu yana kulle.

Ya ce an tura ‘yan sandan ne zuwa ofisoshin jam’iyyar domin hana ‘ya’yan jam’iyyar shiga ofisoshinsu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Sani Kamilu Muhammed, ya ki amsa kiran da aka yi masa, kuma bai amsa sakon wayar da aka aike masa ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 − two =