Ganduje ya bayar da umarnin rusa wani gini a gidan Sheikh Nasiru Kabara

76

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin gaggauta rusa wani gini da ya sabawa doka a gidan Sheikh Nasiru Kabara.

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ba da umarnin ne bayan bincike ya nuna cewa ba a bayar da izini a hukumance ba game da ginin da aka yi a filin masarautar Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar jiya a Kano.

A wani batun kuma, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 19 ga watan Satumba domin yanke hukunci a kan karar da malamin addinin musuluncin nan, Abduljabbar Nasir Kabara, ya shigar a kan gwamnatin jihar Kano da wata kotu, kan zargin cin zarafi.

Mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke ranar a jiya bayan lauyoyin masu shigar da kara sun amince da tsarin nasu tare da gabatar da hujjojin su akan lamarin da kuma rashin amincewarsu.

Abduljabbar Nasir Kabara, ta bakin lauyansa, Shehu Dalhatu, ya kai karar babbar kotun shari’ar musulunchi ta Kofar Kudu da ke Kano da kuma gwamnatin jihar Kano.

2 SHARHOHI

  1. wannan kwaba labarai ne, ba dangantaka tsakanin Abduljabbar da gini…..ko da shariarsa.
    a dinga fayyace labari…..stop misleading people

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five + 1 =