Farouk Adamu Aliyu ya maka APC a kotu

243

Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Jigawa, Honorabul Farouk Adamu Aliyu ya bukaci babbar kotun tarayya da ta dakatar da jam’iyyar daga shiga zaben gwamna mai zuwa na shekarar 2023.

Farooq Aliyu, wanda ya shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar a jihar tare da wasu ‘yan takara, ya sha kaye a hannun mataimakin gwamna na yanzu Malam Umar Namadi.

Tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Kudu/Buji, ya maka jam’iyyar ta APC a kotu, inda ya bukaci ta dakatar da jam’iyyar daga shiga zaben gwamna saboda jam’iyyar ba ta da dan takara.

Ya kuma bukaci kotun da ta tilastawa jam’iyyar ta mayar masa da kudin fom din takararsa na naira miliyan 50 sannan ta biya shi diyyar naira miliyan 500.

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Dutse, babban birnin jiha, ta dage shari’ar bayan ta saurari shaidun masu kara da wadanda ake kara suka gabatar.

Mai shari’a Hassan Dikko da ke jagorantar shari’ar ya dage cigaba da sauraren karar har sai wata rana da za a sanar da bangarorin biyu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 + 4 =