Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa wadanda suka rasa ‘yan uwansu a hare-haren ta’addanci da aka kai a jihohin Sokoto, Kaduna da Filato.
A cikin sakon ta’aziyyar da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar jiya a Abuja, shugaban kasar ya duba halin da ake ciki bayan rahotannin asarar rayuka da dama a hare-haren.
Ya kuma bada tabbacin goyon bayan gwamnatin tarayya ga gwamnatocin jihohin da abin ya shafa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin tarayya ta bai wa jami’an tsaro cikakken ‘yancin tunkarar wadannan hare-hare tare da kawo karshen su.
Shugaban kasar ya ce ya yi Allah wadai da wadannan hare-haren na dabbanci da ake kai wa a kasarnan.
Daga nan sai shugaban kasar ya yi addu’ar samun sauki cikin gaggawa daga Allah ga wadanda suka jikkata a hare-haren.