Buhari ya kaddamar da daftarin kidayar jama’a ta 2023

40
Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da daftarin aikin kidayar yawan jama’a da gidaje na kasa na shekarar 2023, da nufin inganta wayar da kai da fadakar da jama’a kan hanyoyin kidayar ta jama’a.

Ya kaddamar da daftarin ne a taron masu ruwa da tsaki na kasa kan kidayar shekarar 2023, wanda hukumar kidaya ta kasa tare da hadin gwiwar hukumar kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya ta shirya, yau a Abuja.

Shugaban kasar ya ce gudanar da kidayar jama’a da gidaje na shekarar 2023 ya zama wajibi bisa la’akari da bukatar samar da sabbin bayanan yawan al’umma da zamantakewa bisa la’akari da tattalin arzikin kasa.

A cewarsa, bayanan kidayar za su zama ginshikan tsare-tsare na kasa da kuma ci gaba mai dorewa.

Ya kara da cewa gazawar kasarnan wajen gudanar da kidayar jama’a a cikin shekaru 16 da suka gabata ya haifar da tabarbarewar bayanai saboda alkaluman kidaya na karshe da aka gudanar a shekarar 2006 sun dade dayawa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 − 2 =