Badaru, Bagudu, Dangote da BUA sun samu lambar yabo mafi girma a Nijar

48

Shugaban Jamhuryar Nijar Muhammad Bazoum ya baiwa gwamna Muhammad Badaru Abubakar lambar yabo ta girmamawa saboda kishin kasa da gudunmawar da yake bayarwa wajen habaka tattalin arzikin Nijar.

Da yake jawabi yayin mika lambar yabon ga Gwamnan, Shugaba Bozoum ya bayyana shi a matsayin mai gaskiya da ke taimakawa jamhuriyar Nijar da al’ummarta a matakai daban-daban na diflomasiyya.

Muhammad Bazoum ya bayyana kasuwar kan iyaka kan iyaka tsakanin Maigatari da ke jihar Jigawa da kasarsa, wanda Gwamna Badaru Abubakar ya kaddamar a matsayin wani gagarumin yunkuri da ya taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasarsa tare da samar da ayyukan yi ga al’ummar Nijar da dama.

Da yake karbar lambar yabo, Gwamna Badaru Abubakar ya gode wa shugaba Bozoum bisa wannan karramawa da aka yi masa, ya kuma ba shi tabbacin ci gaba da bayar da goyon baya da hadin gwiwar jihar Jigawa da Najeriya baki daya domin inganta huldar diflomasiya da tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.

Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu, da shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da shugaban rukunin kamfanin BUA, Alhaji Abdussamad Isyaku Rabiu, sun samu lambar yabon daga shugaban kasa Muhammad Bazoum.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × three =