ASUU: Za mu janye yajin aiki a yau matukar…

177

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta sha alwashin janye yajin aikin da take gudanarwa a fadin kasarnan muddin gwamnatin tarayya ta biya mata bukatunta yayin zaman ganawar yau.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodoke, shine ya sanar da haka a jiya lokacin da aka zanta da shi a wani shirin gidan talabijin na channels.

Kungiyar malaman tana yajin aiki tun daga ranar 14 ga watan Fabrairun bana, bayan gwamnatin tarayya ta ki amincewa ta biya mata wasu daga cikin bukatunta.

A ranar 19 ga watan Yuli, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da wa’adin makonni biyu ga ministan ilimi ya warware rikicin dake tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayya.

Sai dai duk da kasancewar fadar shugaban kasa ta musanta wannan wa’adin, wata sanarwa a ranar 20 ga watan Yuli da kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya fitar tace za a iya cimma matsaya cikin kwanakin da basu kai haka ba muddin dukkan bangarorin suka bayar da hadin kai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − 19 =