An zargi hukumar tsaron fararen hula civil defense a jihar Bayelsa da karkatar da wata motar dakon man dizal mai lita 45 a jihar.
An rawaito cewa rundunar sojin Najeriya ta cafke motar ne a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, inda aka mika ta ga hukumar ta civil defense domin ci gaba da bincike kan sahihancin man.
Amma watanni bayan mika motar, har yanzu ba a kammala binciken ba.
An bayar da rahoton cewa tuni hukumar ta sayar da man tsakanin ranar 21 zuwa 25 ga watan Yuni tare da cinye kudin.
Wata majiya a hukumar ta jihar ta shaida wa manema labarai cewa kwamandar hukumar, Lucy Fakoye, ta hada baki da wasu ma’aikatanta inda suka tafi da motar zuwa wani waje a jihar Edo suka sayar da man har ma da motar.
A halin da ake ciki kuma, mamallakin man, Muhammad Umar-Idris, ya kai kara ga kwamandan rundunar na kasa, inda ya nemi a biya masa hakkinsa.