An saki karin mutane 5 da aka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna

52

‘Yan ta’addan da suka kai hari tare da yin garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun sake sakin wasu mutane 5 da suka kama.

Sakin na zuwa ne kwanaki kadan bayan ‘yan ta’addar sun sako wasu mutane 4 da suka yi garkuwa da su.

Da yake magana da gidan Talabijin na Channels a jiya, Tukur Mamu, wanda ke shiga tsakani a sasantawa, ya ce ana ci gaba da kokarin ceto sauran wadanda abin ya shafa.

Ya bayyana sunayen mutane biyar da aka saki da Farfesa Mustapha Umar-Imam, wanda likita ne a asibitin koyarwa na Jami’ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto; sai Akibu Lawal, da Abubakar Ahmed-Rufai, da Mukhtar Shu’aibu da Sidi Aminu-Sharif.

Tukur Mamu ya ci gaba da bayyana cewa ya fice daga tattaunawar ne saboda barazanar da ake yi wa rayuwarsa, mutuncinsa da kuma rashin goyon baya daga gwamnatin tarayya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × one =