An fara kada kuri’a a zaben Angola mafi zafi tun bayan yancin kai

34

Ana sa ran zaben Angola a yau zai kasance mafi zafi tun bayan samun ‘yancin kan kasar a shekarar 1975.

Da yake jam’iyya mai mulki ta shafe fiye da shekaru arba’in tana mulki, zai yi wuya a yi tunanin cewa za ta iya rasa matsayinta a kan karagar mulki.

Amma tana fuskantar karuwar rashin jin dadi daga ‘yan kasa sakamakon matsanancin talauci da rashin aikin yi.

Duk da cewa Angola tana da arzikin mai da ma’adanai, da yawan mutanen kasar ba su ci gajiyar wannan arzikin ba.

Bayan maraba da samun shekaru 20 na zaman lafiya bayan dogon yakin basasa, hakan bai samar da nasarorin da mutane da yawa suke fata ba.

Akwai jam’iyyu takwas da suke fafatawa a zaben, amma babbar jam’iyyar hamayya ga jam’iyyar mai mulki ta taba kasancewa wata kungiyar ‘yan tawaye a baya.

Jam’iyyar adawar na neman amfani da rashin jin dadi yayin daga masu jefa kuri’a kusan miliyan 15 ke zaben shugaban kasa da ‘yan majalisa domin wa’adin mulki na shekaru biyar masu zuwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − 10 =