‘Yan gudun hijira na iya shiga Boko Haram saboda talauci – Zulum

38

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana fargabar cewa rashin magance tabarbarewar arziki da talauci na iya tilastawa wasu ‘yan gudun hijira shiga cikin mayakan Boko Haram da na ISWAP.

Gwamnan, ya bayyana hakan ne a jiya a yayin rufe sansanonin ‘yan gudun hijira na Dalori-1, da Dalori-2, da Gubio da Muna da ke Maiduguri, babban birnin jihar.

Ya ce gwamnatin jihar a karkashin mulkinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an sake tsugunar da al’umma cikin mutunci.

Gwamnan ya ce za a rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira kafin karewar wa’adin mulkinsa, yana mai kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bullo da wani tsari mai dorewa domin dakile dogaro da tallafin jin kai da ‘yan gudun hijirar ke yi.

Babagana Zulum ya yaba wa shugaban asusun tallafawa wadanda rikici ya shafa, Janar Theophilus Danjuma mai ritaya, da kuma asusun tare da gwamnatin jihar, bisa bayar da tallafi mafi girma ga wadanda rikici ya shafa a cikin sama da shekaru 13 na rikici.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 3 =