Sojin sama sun jefa bama-bamai bisa kuskure a Katsina

77

Wani jirgin yakin sojin saman Najeriya ya jefa bama-bamai bisa kuskure a kauyen Kunkuna da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina, inda rahotanni suka ce mutane da dama sun mutu.

An bayar da rahoton cewa, jirgin ya kai hari bisa kuskure a wani samame da aka nufi kaiwa sansanonin ‘yan ta’adda a yankin.

Har yanzu dai rundunar sojin Najeriya ba ta ce uffan ba dangane da lamarin.

A ranar 17 ga watan Junairun shekarar 2017 ne jirgin yakin sojojin saman Najeriya ya jefa bam a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Rann na jihar Borno bisa kuskure, inda ya kashe mutane 115 tare da raunata wasu 100.

A shekarar da ta gabata ma wani jirgin saman soji ya kai harin bam a garin Yunusari na jihar Yobe bisa kuskure, inda ya kashe mutane akalla 10.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen + sixteen =