Hukumar raya yankin arewa maso gabas tana shirin gina manyan makarantu guda 18 a shiyyar Arewa maso Gabas na kasarnan.
Manajan Darakta kuma babban jami’in hukumar Mohammed Alkali ne ya bayyana haka a yau a lokacin da yake duba daya daga cikin wuraren da ake gina makarantun a Gashua a Jihar Yobe.
Mohammed Alkali ya ce za a gina kowace daya daga cikin manyan makarantun a mazabu uku na majalisar dattawa cikin jihoshi 6 na yankin Arewa maso Gabas, kuma hakan wani bangaren na shirin samar da cigaba na hukumar.
Manajan daraktan ya bayyana jin dadinsa a lokacin da ya duba ma’aikatu, dakunan shan magani da dakin karatu mai daukar mutane 600 da hukumar ta gina a Gashua.
Tunda farko, Mohammed Alkali ya gabatar da motocin bas masu kujeru 22 da 18 ga jami’ar tarayya ta Gashua a madadin hukumar.
A nata jawabin, mataimakiyar shugabar jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri, ta bayyana jin dadin ta tare da yabawa hukumar bisa kyautar motocin.