Maniyyatan Najeriya sama da 3,600 sun rasa zuwa Hajji

47

Kimanin musulmi miliyan daya ne za su kasance a Arafat a yau, wanda shi ne muhimmin ibadar da musulmi ke gudanarwa yayin aikin hajji a kasar Saudiyya.

Sai dai kimanin ‘yan Najeriya maniyyata 3,660 da suka shirya gudanar da aikin hajjin, suka cire tsammani bayan da jirgin karshe na tawagar Najeriya ya tashi da yammacin jiya, ba tare da sun samu tafiya ba.

Wannan shi ne babban aikin hajjin na farko da ke gudana tun bayan dambarwar da annobar cutar korona ta haifar a farkon shekarar 2020. A shekarar ta 2020 da 2021, tsirarun mazauna Saudiyya ne kawai suka gudanar da aikin hajji.

A bana dai an shirya gudanar da aikin hajjin da ‘yan kasashen waje dubu 850 tare da ‘yan Saudiyya dubu 150. Har yanzu adadin bashi da yawa idan aka kwatanta da kusan mahajjata miliyan biyu da rabi da suka yi aikin hajjin shekarar 2019.

Sau biyu dai Najeriya na samun karin wa’adin kwashen alhazanta bayan ta kasa kammala jigilar maniyyatanta.

An ware wa kasarnan kujerun aikin hajji guda 43,008.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 − 2 =