Na kagu na sauka saboda wahala – Buhari

67

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya kagu ya mika ragamar mulki ga wanda zai gaje shi saboda yana shan wahala.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne jiya a lokacin da ya karbi bakuncin wasu gwamnonin jam’iyyar APC da ‘yan majalisa da shugabannin siyasa a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.

Shugaban kasar ya je Daura ne a ranar Juma’a domin gudanar da bukukuwan Sallah Babba.

Shugaba Buhari ya shaida wa bakinsa da su dage wajen taimaka wa dimbin ‘yan Najeriya da ke neman damammaki.

Shugaban kasar ya shaida wa gwamnonin da shugabannin siyasa cewa kusan shekara guda bai je gidansa da ke Daura ba, saboda yawan aiki.

Shugaba Buhari ya ce zai koma gidansa dake Daura, ba Kaduna ba, inda ya ke da gida mafi kyau.

Dangane da batun tsaro, shugaban kasar ya ce yankin Arewa maso Yamma ya kara haifar da kalubale, kuma an samu wasu nasarori a wasu yankuna.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three + nine =