Masu binciken cuta mai karya garkuwar jiki sun sanar a yau cewa mutum na hudu ya warke daga cutar, amma tsarin da aka warkar da shi da ke da hadari ga marasa lafiyar da ke fama da cutar kansa na iya zama kwanciyar hankali kadan ga dubun-dubatar miliyoyin mutanen da ke dauke da cutar a duniya.
Mutumin mai shekaru 66, mai lakabin majinyacin City of Hope, sunan asibitin da aka yi masa jinya, an ayyana shi a matsayin wanda ya warke gabannin taron kasa da kasa kan cuta mai karya garkuwar jiki wanda za a fara a kasar Kanada ranar Juma’a.
Shi ne mutum na biyu da aka sanar ya warke a bana bayan da masu bincike suka sanar a watan Fabrairu cewa wata mata ‘yar Amurka da aka yiwa lakabi da majinyaciyar New York ita ma ta samu sauki.
Majinyacin City of Hope kamar majinyatan Berlin da Landan da suka riga shi warkewa, ya samu waraka daga cutar bayan da aka yi masa dashen bargo da ake yi don magance cutar kansa.
Wani mutum, majinyacin Duesseldorf, shi ma a baya an ce ya kusa warkewa, wanda ke iya kawo adadin wadanda suka warke zuwa biyar.