Minista yayi watsi da barazanar tsige Buhari

40

Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana barazanar da wasu ‘yan majalisar wakilan kasarnan suka yi na fara shirin tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kalubalen tsaro a fadin kasar nan a matsayin abinda bai dace ba.

Wasu sanatoci daga jam’iyyun adawa da wasu ‘yan jam’iyyar APC mai mulki sun bayyana rashin jin dadinsu kan matsalolin tsaro da kasar ke fama da su, inda suka baiwa shugaban kasar wa’adin makonni shida ya magance matsalar ko kuma ya fuskanci shirye-shiryen tsige shi.

Lai Mohammed, wanda yake amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya jiya a Abuja, ya ce gwamnatin tarayya na aiki ba dare ba rana domin ganin an shawo kan matsalar.

A cewarsa, babu bukatar wannan wa’adi, domin gwamnati na yin duk mai yiwuwa wajen magance matsalolin tsaro a kasarnan.

Ministan ya kuma bayyana barazanar da ‘yan ta’adda ke yi na yin garkuwa da shugaban kasa a matsayin abin dariya kuma farfaganda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 + 5 =