Max Air zai fara dawo da alhazai 16,000 zuwa Najeriya a gobe

75

Daya daga cikin kamfanonin jiragen saman da suke jigilar alhazai a bana, Max Air, ya ce gobe zai fara jigilar alhazai daga Saudiyya zuwa Najeriya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin, Ibrahim Dahiru, ya fitar jiya a Abuja, ta ce alhazan jihar Borno za a fara kwasowa zuwa gida.

Hukumar Alhazai ta kasa ta warewa kamfanin Max Air adadin mahajjata 16,000 daga jihohi 13 domin jigilarsu da dawowa da su gida bayan gudanar da aikin Hajjin bana.

Jihohin sun hada da Borno, Adamawa, Bauchi, Gombe, Jigawa, Taraba, Kogi, Niger, Kwara, Katsina, Benue, Plateau da Nasarawa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven + 2 =