Matsalar karancin abinci ta kunno kai a Najeriya – Majalisa

52

Majalisar wakilai ta koka kan matsalar karancin abinci da ke kunno kai a Najeriya, inda ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fara daukar matakan kariya na gaggawa.

A zamanta na jiya, majalisar ta bukaci fadar shugaban kasa da ma’aikatar noma da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa da su fara shirye-shiryen dakile kalubalen abinci da ya kunno kai.

Wadannan kudurori sun biyo bayan amincewa da wani kudiri na gaggawa mai muhimmaci ga jama’a wanda Rimamnde Shawulu da Solomon Bob suka dauki nauyi.

Da yake gabatar da kudirin, Rimamnde Shawulu yayi nuni da cewa duniya na fargabar fuskantar karancin abinci da yunwa.

Rimamnde Shawulu ya ce majalisar ta lura cewa a wani sabon hasashe, akalla jihohi 16 da babban birnin tarayya za su fuskanci matsalar karancin abinci a shekarar da muke ciki. Ya bayyana cewa jihohin sun hada da Abia, Adamawa, Benue, Cross Rivers, Edo, Enugu, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Lagos, Niger, Plateau, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine + 8 =