Malaman makaranta sun fara yajin aiki a Ghana

58

Malaman makarantun firamare da na sakandare a fadin kasar Ghana sun ce sun shiga yajin aikin saboda ba a biya su alawus-alawus ba.

Sun ce alawus din wanda shine kashi 20 cikin 100 na albashinsu, yana da matukar muhimmanci don rage musu illar matsin tattalin arziki.

An samu hauhuwar farashin kayan masarufi a kasar mafi muni cikin shekaru 18, kuma kasar da ke da arzikin ma’adinai mai yiwuwa nan ba da jimawa ba za ta sami karin rancen kudi don biyan hakkokin ma’aikatan gwamnati.

A wannan makon ne ake sa ran wata tawaga daga asusun lamuni na duniya IMF za ta isa Ghana inda za ta fara tattaunawa da gwamnatin kasar kan shirin bawa kasar bashi.

Ma’aikatan da basa koyarwa su ma sun shiga yajin aikin da aka ayyana jiya.

Yajin aikin na zuwa ne bayan da gwamnatin Ghana ta gaza cika wa’adin ranar 30 ga watan Yuni da shugabannin kungiyoyin suka gindaya yayin tattaunawa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × two =