Majalisar zartarwa ta amince da karin kudi domin kammala aikin hanyar Kano-Katsina

44

Majalisar zartarwa ta tarayya a jiya ta amince da karin kudi naira miliyan dubu 16 domin kammala aikin babban titin Kano zuwa Katsina.

Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron majalisar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ministan ya ce an kara kudin kwangilar kwangilar ne da naira miliyan dubu 16, wanda ya kara ainihin kudin kwangilar daga naira miliyan dubu 29 zuwa naira miliya dubu 46.

Ministan ya kuma shaidawa manema labarai cewa an amince da kudi sama da naira miliyan 800 domin siyan motocin aiki guda 32 ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.

A nasa bangaren, ministan ma’adinai da karafa, Olamilekan Adegbite, ya shaida wa manema labarai cewa majalisar ta amince da wani kudiri kan ma’adinai.

Ya bayyana cewa kudirin zai rage fitar da tama zuwa kasashen waje ta yadda Najeriya za ta ci gajiyar sarrafa shi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × four =