Majalisa ta gayyaci gwamnan CBN saboda faduwar darajar naira

41

A wani labarin mai alaka da wannan, Majalisar Dattawa ta gayyaci gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele, kan faduwar darajar Naira.

Hakan ya biyo bayan kudirin da Sanata Olubunmi Adetunmbi na jam’iyyar APC daga jihar Ekiti ya gabatar.

Naira a halin yanzu ana cinikinta a tsakanin 690 zuwa 700 kowace dala a kasuwannin bayan fage.

Da yake bayar da gudunmawa a muhawarar, sanata mai wakiltar jihar Neja ta Gabas, Sani Musa, ya ce Naira za ta kara daraja ne kadai idan muna cinye abin da muka noma.

A nata bangaren, Sanata mai wakiltar jihar Ekiti ta Kudu, Biodun Olujimi, ta zargi babban bankin kasa da daukar nauyin kare Naira.

Majalisar dattijai ta bukaci bankin na CBN da ya dakatar da faduwar darajar Naira cikin sauri.

An amince da kudirin ne bayan shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya nemi a kada kuri’a.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × four =